Mar 19, 2019 06:20 UTC
  • Shugaban AU Ya Bukaci Daukar Matakan Hana Aukuwar Tashe-tashen Hankula A Afrika

Shugaban kungiyar tarayya Afrika, na wannan karo, kana shugaban kasar Masar Abdel-Fattah al-Sisi ya bukaci kwamishinan kungiyar, Moussa Faki, da a dauki kwararan matakan rigakafin tashe tashen hankula domin bunkasa cigaban nahiyar Afrika cikin sauri.

Shugaba Al'Sisi, wanda ya karbi shugabancin kungiyar ta AU a watan Fabrairu, yayi wannan tsokaci ne a lokacin ganawarsa da Faki a gefen taron dake gudana na dandalin hadin kan matasan kasashen Larabawa da na Afrika a lardin Aswan dake kasar Masar.

Shugaban kasar Masar ya bayyana cewa kasarsa a shirye take ta cigaba da yin hadin gwiwa da kuma jagorancin hukumar gudanarwar kungiyar ta AU wajen yin aikin tabbatar da hadin kan kasashen Afrika a dukkan fannoni a lokacin wa'adin jagorancinsa na kungiyar ta AU.

A lokacin ganawar, Sisi ya jaddada muhimmancin amfani da kwararan matakai da nufin cimma muhimman nasarori mafiya muhimmanci, musamman a fannin cigaban tattalin arzikin nahiyar, da samar da zaman lafiya da tsaro, da kyautata tsarin shugabancin kungiyar AU da karfafa hadin gwiwa tsakanin kungiyar AU da sauran abokan hulda na kasa da kasa.

Tags