Mar 23, 2019 06:41 UTC
  • MDD, Ta Bukaci A kara Kai Dauki A Gabashin Afrika Bayan iftila’in, Guguwar Idai

Babban sakatare na MDD, Antonio Guteres, ya bukaci kasashen duniya dasu kara kaimi wajen samar da tallafi ga dubban mutanen da ifti’la’in mahaukaciyar guguwar nan ta Idai ya shafa a gabashin Afrika.

A cikin sanarwar da ya sanya wa hannu, babban sakataren na MDD, ya ce, ya kamata mu kara himma wajen taimaka wa al’ummar kasashen Mozambique, Malawi da kuma Zimbabwe.

A cewarsa MDD, ta ware dalar Amurka Miliyan ashirin a matsayin tallafin gaggawa na farko, amma duk da hakan ana da matukar bukatar tallafi daga sauren kasashen duniya.

A halin da ake ciki alkalumman wucin gadi na barna da hasara da aka fitar bayan guguwar ta Idai, sun ce mutum 259 ne suka rasa rayukansu a Zimbabwe, sai kuma 257 da suka bata.

 A Mozambique kuwa adadin mutanen da aka bayyana sun rasa rayukansu a hukumance ye zuwa jiya Juma’a sun kai 242, a yayin da wasu daruruwan mutane suka bata.

 

Tags