Yan Tawayen Yankin Darfur Na Kasar Sudan Sun Sanar Da Rungumar Shirin Dakatar Da Bude Wuta
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i25959-yan_tawayen_yankin_darfur_na_kasar_sudan_sun_sanar_da_rungumar_shirin_dakatar_da_bude_wuta
Kungiyoyin 'yan tawayen yankin Darfur da ke yammacin kasar Sudan guda uku sun sanar da shirinsu na rungumar yarjejeniyar dakatar da bude wuta na tsawon watanni biyu da nufin bada damar isar da kayayyakin jin kai ga al'ummar yankin da yaki ya wurga cikin mummunan hali.
(last modified 2018-08-22T07:01:05+00:00 )
Dec 02, 2017 15:34 UTC
  • Yan Tawayen Yankin Darfur Na Kasar Sudan Sun Sanar Da Rungumar Shirin Dakatar Da Bude Wuta

Kungiyoyin 'yan tawayen yankin Darfur da ke yammacin kasar Sudan guda uku sun sanar da shirinsu na rungumar yarjejeniyar dakatar da bude wuta na tsawon watanni biyu da nufin bada damar isar da kayayyakin jin kai ga al'ummar yankin da yaki ya wurga cikin mummunan hali.

Kamfanin dillancin labaran kasar China na Xin Huwa ya watsa rahoton cewa: Shugabannin kungiyoyin 'yan tawayen yankin Darfur da ke yammacin kasar Sudan guda uku wato kungiyar Sudan Liberation Movement-Transitional Council {SLM-TC} da Justice and Equality Movement {JEM} da kuma SLM-Minni Minnawi sun rattaba hannu kan amincewa da yarjejeniyar dakatar da bude wuta na tsawon watanni biyu da ta fara daga jiya Juma'a 1 ga watan Disamba zuwa 31 ga watan Janairun shekara ta 2018 mai zuwa.

Kungiyoyin uku sun bayyana cewa sun amince da yarjejeniyar ce da nufin ganin an isar da kayayyakin jin kai ga al'ummar yankin na Darfur da suke cikin halin kaka-ni ka yi amma a shirye suke su maida da martani kan sojojin gwamnatin Sudan matukar suka fuskanci harin wuce gona da iri. 

Tun a shekara ta 2003 ce gwamnatin Sudan ta fara yaki da kungiyoyin 'yan tawayen yankin Darfur da ke yammacin kasar bayan da suke shelanta yaki kanta sakamakon zargin maida yankin saniyar ware a kasar.