Sudan Ta Kudu: An Cimma Yarjejeniyar Tsagaita Wuta Tsakanin Gwamnati Da 'Yan Tawaye
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i26583-sudan_ta_kudu_an_cimma_yarjejeniyar_tsagaita_wuta_tsakanin_gwamnati_da_'yan_tawaye
Kamfanin dillancin labarun Farasna ya nakalto cewa; An cimma yarjejeniyar ne a karkashin shiga tsakanin kungiyar Igad a birnin Adas Ababa na kasar Habasha.
(last modified 2019-08-10T10:24:46+00:00 )
Dec 22, 2017 02:53 UTC
  • Sudan Ta Kudu: An Cimma Yarjejeniyar Tsagaita Wuta Tsakanin Gwamnati Da 'Yan Tawaye

Kamfanin dillancin labarun Farasna ya nakalto cewa; An cimma yarjejeniyar ne a karkashin shiga tsakanin kungiyar Igad a birnin Adas Ababa na kasar Habasha.

Za a fara aiki da yarjejeniyar tsagaita wutar yakin ne tsakanin sojojin gwamnatin Sudan ta kudu da kuma 'yan tawaye daga ranar 24 ga watan nan na Disamba.

Har ila yau an kira yi dukkanin bangarorin biyu da su kaucewa kai wa fararen hula hari, haka nan kuma su rika bada dama ga kungiyoyin agaji su isa ga mabukata.

Tun a 2013 ne dai aka fara yakin basasa a kasar ta Sudan ta kudu a tsakanin sojojin dake biyayya ga shugaba Silva Kiir da tsohon mataimakinsa Reick Machar.