Majalisar Musulmin Kenya Ta Nuna Damuwa Kan Karuwar Cin Hanci Da Rashawa A Kasar
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i32647-majalisar_musulmin_kenya_ta_nuna_damuwa_kan_karuwar_cin_hanci_da_rashawa_a_kasar
Majalisar musulmin kasar Kenya ta nuna matukar damuwa dangane da karuwar ayyukan cin hanci da rashawa a kasar.
(last modified 2018-08-22T07:02:12+00:00 )
Aug 06, 2018 01:21 UTC
  • Majalisar Musulmin Kenya Ta Nuna Damuwa Kan Karuwar Cin Hanci Da Rashawa A Kasar

Majalisar musulmin kasar Kenya ta nuna matukar damuwa dangane da karuwar ayyukan cin hanci da rashawa a kasar.

Shafin yada labarai na standard media ya habarta cewa, majalisar musulmin kasar Kenya ta nuna matukar damuwa dangane da karuwar ayyukan cin hanci da rashawa a kasar a cikin lokutan baya-bayan nan.

Wannan ya zo ne bayan wani zama da mambobin majalisar suka gudanar, inda suka bukaci gwamnatin kasar ta Kenya da ta dauki tsauraran matakai na shiga kafar wando daya da duk wanda aka samu da laifin barnata dukiyar kasa, ko halasta kudin haram, ko karbar cin hanci da rashawa.

Alhaj Shaban Bakari, shugaban majalisar musulmin ya bayyana cewa, musulmin Kenya suna goyon bayan daukar duk wani mataki da gwamnati za ta yi na yaki da cin hanci da rashawa da wwure kudaden jama’a, domin hakan ya bayar da damar habbaka tattalin arzikin kasar.