Mahukunta A Kenya Sun Kori Wani Dan Kasar China Da Ya Kira Mutanen Kasar Da 'Birrai'
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i33074-mahukunta_a_kenya_sun_kori_wani_dan_kasar_china_da_ya_kira_mutanen_kasar_da_'birrai'
Mahukunta a kasar Kenya sun kori wani dan kasar China mai suna Liu Jiaqi daga kasar bayan wani faifan bidiyo da yayi kuma ya watsa yana bayyana al'ummar kasar ciki kuwa har da shugaba Uhuru Kenyatta a matsayin birrai.
(last modified 2018-09-06T12:11:04+00:00 )
Sep 06, 2018 12:11 UTC
  • Mahukunta A Kenya Sun Kori Wani Dan Kasar China Da Ya Kira Mutanen Kasar Da 'Birrai'

Mahukunta a kasar Kenya sun kori wani dan kasar China mai suna Liu Jiaqi daga kasar bayan wani faifan bidiyo da yayi kuma ya watsa yana bayyana al'ummar kasar ciki kuwa har da shugaba Uhuru Kenyatta a matsayin birrai.

Kafar watsa labaran Africanews ta bayyana cewar a faifan bidiyon an jiyo Mr. Jiaqi wanda dan kasuwa ne da ke kasuwanci babura a kasar Kenyan yana bayyana al'ummar Kenya a matsayin birrai, bakaken fata masu warin jiki ga bakin talauci, lamarin da ya fusata mahukuntan kasar saboda wadannan kalamai na nuna wariyar launin fata da yayi.

Hukumar shige da fice ta kasar Kenya ta tabbatar da wannan labarin inda ta ce tuni aka kama mutumin, inda aka soke masa takardar izinin zaman kasar Kenyan sannan kuma yau da rana aka yi waje da shi da korarsa zuwa kasarsu.

Rahotanni sun ce wani ma'aikacin kamfanin dan kasar Chinan wanda yake shirin korarsa ne ya dauki faifan bidiyon mutumin a lokacin da yake wadannan maganganu na batanci wanda ya bata ran al'ummar kasar Kenyan.