Gwamnatin Sudan Ta Kudu Ta Saki Wani Babban Na Hannun Damar Riek Machar
Gwamnatin Sudan ta Kudu ta saki wani babban na hannun damar tsohon madugun 'yan tawayen kasar daga gidan kurkuku a karkashin yarjejeniyar sulhu da aka cimma a kasar.
Mahukunta a Sudan ta Kudu a jiya Asabar sun sanar da sakin William John Endley babban na hannun damar tsohon madugun 'yan tawayen kasar kuma lauyansa daga gidan kurkuku a karkashin yarjejeniyar sulhun da aka cimma a kasar da ta kawo karshen yakin basasa a Sudan ta Kudu.
Kotu a birnin Juba fadar mulkin Sudan ta Kudu a watan Fabrairun wannan shekara ta 2018 ce ta yanke hukuncin kisa kan William John Endley lauyar tsohon madugun 'yan tawayen kasar kan zargin cin amanar kasa da kulla makarkashiyar kifar da gwamnatin shugaba Silva Kiir.
Mahukuntan Sudan ta Kudu sun bayyana cewa; Sakin Wiliam John yana daga cikin irin kyakkyawar niyyar gwamnatin Silva Kiir na ganin ta aiwatar da yarjejeniyar sulhun da aka cimma tsakanin bangarorin siyasar kasar da nufin kawo karshen duk wasu tashe-tashen hankula a Sudan ta Kudu.