Masar Ta Ce Ta Kame Wasu Gungun Mutane Da Suke Shirin Kashe Yarima Mai Jiran Gado Na Saudiyya
Majiyar tsaron Masar ta sanar da cewa: Jami'an tsaron kasar sun kame wani gungun mutane 20 da suke shirya makarkashiyar aiwatar da kisan gilla kan yarima mai jiran gado na Saudiyya Muhammad bin Salman.
Jaridar Alfajr ta kasar Masar ta nakalto daga majiyar tsaron kasar cewa: Jami'an tsaron Masar sun yi nasarar kame wani gungun mutane 20 a lardin Sina ta Arewa na kasar da suka hada da 'yan asalin Masar da baki 'yan kasashen waje suna shirya makarkashiyar aiwatar da kisan gilla kan yarima mai jiran gado na Saudiyya Muhammad bin Salman.
Majiyar ta kara da cewa: Bayan gudanar da bincike kan mutanen sun yi furuci da aniyarsu ta gudanar da wannan makarkashiya, kuma tuni Abbas Kamel shugaban hukumar leken asirin kasar Masar ya sanar da mahukuntan Saudiyya wannan batu a ziyarar aikin da ya kai birnin Riyadh na Saudiyya.
Yarima mai jiran gadon sarautar Saudiyya Muhammad bin Salman ya fara shahara da bakar siyasar murkushe 'yan adawar kasarsa tare da fuskantar suka a duniya musamman matakin da ya dauka na kaddamar da hare-haren wuce gona da iri kan al'ummar Yemen.