MDD: Babu Tabbas Kan Dorewar Sulhu Da Zaman Lafiya A Sudan Ta Kudu
Mataimakin babban sakataren MDD na sashen tabbatar da zaman lafiya ya bayyana cewa sulhu da zaman lafiya a kasar Sudan ta kudu suna cikin halin rashin tabbasa.
Kamfanin dillancin labaran Xinhuwa na kasar China ya nakalto Jean-Pierre Lacroix mataimakin babban sakataren MDD na sashen sulhu da tabbbatar da zaman lafiya yana fadar haka a jiya jumma'a.
Ya kuma kara da cewa matukar yan tawayen a kasar basu ajiye makamansu ba to kuwa babu tabbas kan cewa sulhuntawan da aka cimma tsakanin bangarorin biyu zai dore.
A cikin watan satumba na wannan shekara ta 2018 ne shugaban yan tawayen Sudan ta Kudu Riek Marcher ya rattaba hannu kan yerjejeniyar sulhu da gwamnatin kasar sannan aka amince masa ya sake komawa kan kujerarsa ta mataimakin shugaban kasa. Amma ba'a yi maganan kwance damarar mayakan yan tawayen ba.