MDD Ta Yi Tir Da Cin Zarafin Mata Ta Hanyar Fyade A Sudan Ta Kudu
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i34321-mdd_ta_yi_tir_da_cin_zarafin_mata_ta_hanyar_fyade_a_sudan_ta_kudu
Majalisar Dinkin Duniya, ta bukaci hukumomin Sudan Ta Kudu, dasu gudanar da mutanen da ake zargi da cin zarafin mata ta hanyar fyade a gaban kotu.
(last modified 2018-12-04T00:48:07+00:00 )
Dec 04, 2018 00:48 UTC
  • MDD Ta Yi Tir Da Cin Zarafin Mata Ta Hanyar Fyade A Sudan Ta Kudu

Majalisar Dinkin Duniya, ta bukaci hukumomin Sudan Ta Kudu, dasu gudanar da mutanen da ake zargi da cin zarafin mata ta hanyar fyade a gaban kotu.

Kimanin mata da 'yan mata 150 ne aka rawaito cewa, wasu masu dauke da makamai ciki har da masu sanye da uniform sunyi wa fyade a kasar.

Wata sanarwa da kungiyoyin agaji uku na MDD, da suka hada da UNICEF, da kuma UNFPA suka fitar sun bukaci hukumomin na Sudan ta Kudu dasu yi allawadai da wannan al'amari tare da gurfanar da duk wadanda aka samu da aikata laifin.

Wani rahoto da kungiyar likitoci marar iyaka ta MSF ta fitar a ranar Juma'a data gabata ya nuna cewa mata da 'yan mata 125 ne na Sudan ta Kudun aka ci zarafinsu ko akayi wa fyade a cikin kwanaki goma da suka gabata a daidai lokacinda suke neman abinci na tallafi da hukumomin agaji na kasa da kasa ke bayar wa a birnin Bentiu dake arewacin kasar.