Mar 20, 2019 08:55 UTC
  • PDP Za Ta Gabatar Da Shedu Sama Da 400 A Gaban Kotu Kan Zaben Shugaban Kasa

Dan takarar jam'iyyar shugabancin kasa a karkashin inuwa Jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya wanda ya fadi a zaben shugaban kasa, zai gabatar da shedu sama da 400 domin bayar da sheda kan korafe-korafen magudi da jam'iyyar ke zargin a tafka a zaben.

A lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai jiya a birnin Abuja, shugaban tawagar lauyoyin Alh. Atiku Abubakar dan takarar jam'iyyar shugabancin kasa a karkashin inuwa Jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya, Emmanuel Enoidem, ya bayyana cewa akwai kwararan dalilai, da kuma daruruwan shedu da za su gabatar wa kotu, wadanda suke tabbatar da cewa an tafka magudi a zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar 23 ga watan fabrariru a Najeriya.

Tun bayan da hukumar zaben zaben Najeriya ta sanar da Muhammadu Buhari shugaba mai ci, kuma dan takarar shugabancin kasar karkashin inuwar jam'iyyar APC  a matsayin wanda ya lashe zaben, jam'iyyar PDP ta nuna rashin amincewarta da hakana.

Jam'iyyar PDP ta ce an yi amfani da hanyoyi na yaudara ko tayar da hankula ko batun na'urar zabe wajen wajen aikata magudi, wanda kuma za su tabbatar da cewa sun kalubalanci hakan a kotu bisa kwararan hujjojin da suka ce suna da su.