A. Larijani: Gwamnatin Saudiyya Ita Ce Ummul Aba'isin Matsalolin Da Duniyar Musulmi Suke Ciki
Alkalin alkalai kana shugaban Ma'aikatar shari'a ta Iran, Ayatullah Sadiq Amoli Larijani ya bayyana cewar mahukutan Saudiyya suna amfani da kudaden da suke samu daga man fetur wajen haifar da matsaloli masu yawan gaske ga al'ummomin kasashen Afghanistan, Pakistan, Iraki, Siriya, Labanon da wasu kasashen Afirka.
Ayatullah Sadiq Amoli Larijani ya bayyana hakan ne a yayin da yake jawabi wajen taron manyan jami'an ma'aikatar shari'ar ta Iran a yau din nan Litinin inda ya ce: Abubuwan da Saudiyya ta ke yi wajen yada akidar salafanci da akidar kafirta musulmi sun haifar da fitinu da bala'oi ga duniyar musulmi.
Har ila yau Ayatullah Larijani yayi ishara da irin ayyukan ta'addanci da kisan gillan da gwamnatin Saudiyya take yi inda yace: Babban aikin da Saudiyyan take yi shi ne yada ta'addanci a duniya ciki kuwa har da irin goyon baya na kudi da addini da take ba wa kungiyoyin ta'addanci irin su Al-Qa'id da Daesh.
Alkalin alkalan na Iran ya ce irin kisan gillan da mahukutan Saudiyyan suka yi wa dan jaridar kasar mai sukar gwamnati Jamal Khashoggi wani lamari ne da ke nuni da asalin yanayi da kuma tushen masarautar Saudiyyan yana mai watsi da bayanin da gwamnatin Saudiyyan ta yi dangane da batun mutuwar dan jaridar.