Rahoto: Yunkurin Saudiyya Na Rusa Tattalin Arzikin Iran Da Kashe Wasu Manyan Jami'anta
A cikin wani rahoto da jaridar New York Times ta buga, ta fallasa wani boyayyen shiri da gwamnatin Saudiyya take da shi kan rusa tattalin arzikin kasar Iran, da kuma yi wa wasu daga cikin manyan jami'an kasar ta Iran kisan gilla, musamman ma janar Qasem Sulaimani, babban kwamandan rundunar Quds, reshen dakarun kare juyin juya hali da ke gudanar da ayyuka awajen kasar ta Iran, wanda ya taka gagarumar rawa wajen karya lagon 'yan ta'addan takfir masu da'awar jihadi a kasashen Syria da Iraki.
Jaridar New York Times ta ce; an gudanar da zaman tattaunawa kan wannan batu ne a cikin watan Maris na shekara ta 2017, bayan wata ganawa da ta gudana a birnin Riyadh tsakanin yarima Muhammad Bin Salman, da kuma George Nader, wani dan kasuwa ba'amurke dan asalin kasar Lebanon, wanda yake da alaka ta kai tsaye da fadar White House a Amurka.
Bisa wannan rahoto, an gudanar da zaman tattauna wannan batu da kuma yadda za a aiwatar da shi ne tsakanin Janar Ahmad Asiri, babban jami'in soja da kuma ayyukan leken asiri a kasar Saudiyya, da kuma George Nader, sai kuma Joel Zamel, wanda bayahuden Isra'ila ne kuma dan kasuwa, wanda yake da alaka mai karfi da hukumomin liken asiri na Isra'ila.
Jaridar New York Times ta ce; a lokacin da wadannan bangarori uku suka tattauna wannan batu, dukkanin bangarorin uku sun amince kan yin aiki domin rusa tattalin arzikin kasar Iran, amma kan batun aiwatar da kisan gilla a kan jami'an na Iran, Nader da Zamel sun bukaci yin shawara tare da neman amincewar gwamnatin Trump a kan hakan, amma kuma a lokacin Joel Zamel ya gabatar da shawara kan a tuntubi wani kamfani da ke kasar Birtaniya da ke gudanar da irin wadannan ayyuka, da kuma kamfanin Black Water.
Haka nan kuma Janar Ahmad Asiri ya sanar da su cewa; Saudiyya ta ware dala biliyan biyu domin gudanar da wannan muhimmin aiki.
Jaridar ta fitar da wannan rahoto ne a halin yanzu da ake batun kisan gillar da jami'an tsaron Saudiyya suka yi wa dan jaridar kasar Jamal Khashoggi ne, tare da yin nuni da cewa tun kafin wannan lokacin daa yarima Muhammad Bin Salman na da wani tsararren shiri na aiwatar da wasu ayyukan kisan gilla a wajen kasar ta Saudiyya a kan wasu mutane na musamman, wadanda yake kallonsu a matsayin barazana a gare shi, wanda kuma kisan gillar da aka yi Jamal Kahshoggi daya ne daga cikin abubuwan da shirin na Bin Salman ya kunsa.
A nata bangaren gwamnatin kasar Iran a ta bakin ministan harkokin wajen kasar Muhammad Jawad Zarif, Iran tana da cikakkiyar masaniya kan wannan shiri na Saudiyya, kuma tun a lokacin tana sanya ido a kan dukkanin abubuwan da suke kai da komowa.
Har yanzu dai gwamnatin kasar ta Saudiyya taki ta uffan uffan a kan wannan rahoto da jaridar ta New York Times ta buga, lamarin da masana da dama suke ganin lallai akwai alamar tambaya a kan hakan.