Iran: Mamayar Yankunan Palastinawa Da 'Isra'ila' Ta Yi Shi Ne Tushen Rikici A Gabas Ta Tsakiya
Ofishin jakadancin Iran na dindindin a Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana mamayar da 'Isra'ila' ta yi wa yankunan Palastinawa a matsayin tushen rikicin da ke faruwa a yankin Gabas ta tsakiya.
Mataimakin jakadan Iran na dindindin a MDDn Es'haq Al-e Habib, ne ya bayyana hakan a yayin da yake magana kan nuna rashin amincewa da daftarin kudurin da Amurka ta gabatar da bukaci a yi Allah wadai da kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas.
Mataimakin jakadan na Iran ya ce: An gina daftarin kudurin ne bisa yaudara don kuwa ya rufe ido kan asalin tushen rikicin da ke faruwa a yankin Gabas ta tsakiyan wanda shi ne haramtacciyar mamayar da 'Isra'ila' take yi wa yankunan Palastinawa na tsawon shekaru.
Jam'in diplomasiyyar na Iran ya ci gaba da cewa wannan daftarin kudurin yana nuni da irin yanayin siyasar wajen Amurka ne kan abin da ya shafi al'ummar Palastinu wanda ke cike da yaudara da goyon bayan bangare guda bugu da kari kan rufe ido kan hakkokin Palastinu.
A jiya ne dai aka kada kuduri kan kudirin da Amurka ta gabatar na bukatar yin allawadai da kungiyar ta Hamas, to sai dai kuma ya kasa samun karbuwa a majalisar dinkin duniya.