Iran: Idan HKI Ta Kuskura Ta Fara Wani Yaki A Yanki Zata Jawa Shafe Kanta Daga Doron Kasa
https://parstoday.ir/ha/news/iran-i34983-iran_idan_hki_ta_kuskura_ta_fara_wani_yaki_a_yanki_zata_jawa_shafe_kanta_daga_doron_kasa
Mataimakin babban komandan dakarun kare juyin juya halai a nan JMI Janar Husain Salami ya bayyana cewa idan HKI ta kuskura ta fara wani sabon yaki a halin da ake ciki to kuwa zata fara yakin da zai shafeta a doron kasa da kanta.
(last modified 2019-01-28T08:25:37+00:00 )
Jan 28, 2019 08:25 UTC
  • Iran: Idan HKI Ta Kuskura Ta Fara Wani Yaki A Yanki Zata Jawa Shafe Kanta Daga Doron Kasa

Mataimakin babban komandan dakarun kare juyin juya halai a nan JMI Janar Husain Salami ya bayyana cewa idan HKI ta kuskura ta fara wani sabon yaki a halin da ake ciki to kuwa zata fara yakin da zai shafeta a doron kasa da kanta.

Majiyar muryar JMI ta nakalti Janar Husain Salami yana fadar haka a yau Litinin ya kuma kara da cewa, ko wa ya sani manufar JMI ita ce shafe HKI daga doron kasa don haka idan yahudawan sun soma wani yaki a halin yan a yankin gabas ta tsakiya alamace JMI zata kaiga manufarta na shafi haramtaciyyar kasar daga doron kasar.

Janar Salami yana maida martani ne ga sanarwan da HKI ta bayar na cewa zata kai hare-hare kan sansanonin sojojin kasar Iran da suke cikin kasar Siriya don tilasta mata ficewa daga kasar..

A cikin yan kwanakin da suka gabata ne Firai Ministan HKI Benyamin Natanyahu ya bayyana cewa idan kasar Iran bata kwace sojojita da fice daga kasar Siriya ba zai ci gaba da kai hare-hare kan sansanonin sojojin Iran da suke cikin kasar.