Hukumar Palasdinawa Ta Yi Allah Wadai Da Ci Gaba Da Mamaye Yankunan Palasdinawa
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i33819-hukumar_palasdinawa_ta_yi_allah_wadai_da_ci_gaba_da_mamaye_yankunan_palasdinawa
Ma'aikatar harkokin wajen hukumar cin kwarya-kwaryar gashin kan Palasdinawa ta yi Allah wadai da shirin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila na gina dubban gidajen Yahudawan Sahayoniyya a gabashin birnin Qudus.
(last modified 2018-10-28T15:45:10+00:00 )
Oct 28, 2018 15:45 UTC
  • Hukumar Palasdinawa Ta Yi Allah Wadai Da Ci Gaba Da Mamaye Yankunan Palasdinawa

Ma'aikatar harkokin wajen hukumar cin kwarya-kwaryar gashin kan Palasdinawa ta yi Allah wadai da shirin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila na gina dubban gidajen Yahudawan Sahayoniyya a gabashin birnin Qudus.

A bayanin da ma'aikatar harkokin wajen hukumar cin kwarya-kwaryar gashin kan Palasdinawa ta fitar a yau Lahadi: bayanin yana dauke da yin tofin Allah tsine kan matakin da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ta dauka na gudanar da gine-ginen gidajen Yahudawan Sahayoniyya 'yan kaka gida guda 20,000 a yankin Ma'ale Adumim a shiyar gabashin birnin Qudus.

Kungiyoyin kasa da kasa sun sha jaddada cewa: Gudanar da gine-ginen matsugunan Yahudawa Sahayoniyya 'yan kaka gida a yankunan Palasdinawa da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ta mamaye a yankunan gabar yammacin kogin Jordan da Baitul-Muqaddas basu kan doka, kamar yadda kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya a ranar 23 ga watann Disamban shekara ta 2016 ya sake jaddada haramcin mamaye yankunan Palasdinawa musamman gudanar da gine-ginen matsugunan Yahaudawan Sahayoniyya 'yan kaka gida a cikinsu.