Hazim: Saudiyya Ta Kashe Jamal Khashoggi Ne Domin Tsoron Fallasa Asiranta
Daraktan jaridar Alfajr ta kasar Aljeriya Haddad Hazim ya bayyana cewa, mahukuntan kasar Saudiyya sun dauki matakin kashe Jamal Khashoggi ne domin tsoron kada ya fallasa asiransu da ya sani.
A lokacin da yake zantawa da kamfanin dillancin labaran IRNA a jiya, Haddad Hazim ya bayyana cewa, Jamal Khashoggi ya kasance mai bada shawara ga tsohon shugaban hukumar leken asiri ta kasar Saudiyya Turki Faisal, a kan hakan ya san asirai masu tarin yawa wadanda zai iya fallasa Saudiyya a kansu a halin yanzu, da hakan ya hada har da batun hannun da Saudiyyah take da shi a harin 11 ga watan Satumba a kasar Amurka.
Hazim ya kara da cewa, duk da yake wannan ba shi ne karon farko da yarima Muhammad Bin Salman ke kashe masu adawa da shi ba, amma batun Khashoggi lamari ne mai matukar hadari ga masarautar Saudiyya, a kan haka ne suka gaggauta kawar da shi ta hanyar yi masa kisan gilla.
Hazim ya ce duk da cewa kisan Khashoggi mummunan aiki da ya cancanci yin Allawadai, amma kuma a lokaci bai kamata a manta da laifukan yaki da kisan gillar da masarautar saudiyya take ci gaba da yi kan dubban fararen hula mata da kanan yara a kasar Yemen ba.
Jami'an tsaron Saudiyya na musamman ne dai suka aiwatar da kisan Jamal Khasoggi a cikin a cikin karamin ofishin jakadancin Saudiyya da Istambul a kasar Turkiya a ranar 2 ga watan Oktoban da ya gabata, Saudiyya ta karyata batun daga farko, amma bayan matsin lambar kasashen duniya ta fito ta amince da kisan nasa.