Wani Bapalasdine Ya Yi Shahada Sakamakon Harin Sojojin H.K.I Kan Yankin Zirin Gaza
Wani bapalasdine ya yi shahada sakamakon harin wuce gona da iri da sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila suka kai kan yankin Zirin Gaza na Palasdinu.
Mijiyar asibitin Palasdinu a jiya Alhamis ta sanar da cewa: Sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila sun kaddamar da harin wuce gona da iri kan yankin Al-Wusda da ke gabashin Al-Maghazi a tsakiyar Zirin Gaza, inda suka jikkata Palasdinawa masu yawa, kuma bayan janyewarsu daga yankin daya daga cikin Palasdinawan da suka samu raunuka ya yi shahada.
Tun a cikin watan Maris na wannan shekara ce al'ummar Palasdinu suka fara zanga-zangar lumana domin neman hakkin Palasdinawa 'yan gudun hijira komawa kasarsu ta gado lamarin da ya tunzura gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila wajen yin amfani da karfi domin murkushe zanga-zangar amma har yanzu hakarta bata kai ga ruwa ba.