Wani Matashin Bapalasdine Ya Yi Shahada Bayan Jikkata Sojojin HKI Biyar A Birnin Qudus
Wani matashin Bapalasdine ya farma sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila da wuka a birnin Qudus, inda ya jikkata sojoji biyar, sannan ya yi shahada sakamakon harbinsa da bindiga.
Tashar talabijin ta Al-Manar da ke kasar Lebanon ta watsa rahoton cewa: Wani matashin Bapalasdine ya yi shahada sakamakon harbinsa da bindiga bayan ya yi nasarar jikkata sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila guda biyar a birnin Qudus na Palasdinu da aka mamaye.
Matashin Bapalasdine ya farma sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ne da wuka a matsayin maida martani kan hare-haren wuce gona da iri da sojojin suke kai wa kan al'ummar Palasdinu musamman a yankin Zirin Gaza lamarin da ke janyo shahadar Palasdinawa tare da jikkata wasu da dama a kullum rana.