Yan Siyasar Mauritaniya Sun Yi Allah Tsine Da Harin Wuce Gona Da Irin HKI Kan Yankin Palasdinu
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i34104-yan_siyasar_mauritaniya_sun_yi_allah_tsine_da_harin_wuce_gona_da_irin_hki_kan_yankin_palasdinu
Jam'iyyar Rafah ta kasar Mauritaniya ta yi Allah wadai da bakar siyasar gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila kan yankin Zirin Gaza na Palasdinu.
(last modified 2018-11-15T15:26:51+00:00 )
Nov 15, 2018 15:26 UTC
  • Yan Siyasar Mauritaniya Sun Yi Allah Tsine Da Harin Wuce Gona Da Irin HKI Kan Yankin Palasdinu

Jam'iyyar Rafah ta kasar Mauritaniya ta yi Allah wadai da bakar siyasar gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila kan yankin Zirin Gaza na Palasdinu.

A bayanin da jam'iyyar Rafah ta Mauritaniya ta fitar yana dauke da yin tofin Allah tsine kan matakan wuce gona da irin da sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila suke dauka kan yankin Zirin Gaza na Palasdinu tare da yin Allah wadai kan shirun da kasashen Larabawa suka yi kan irin wannan bakar siyasa ta zalunci.

Bayanin jam'iyyar ta Rafah ya kara da jaddada matsayin jam'iyyar na goyon bayan al'ummar Palasdinu da kungiyoyin gwagwarmayar Palasdinawa da suke ci gaba da yin tsayin daka wajen fuskantar bakar siyasar zaluncin yahudawan sahayoniyya 'yan mamaya.

Har ila yau jam'iyyar ta Rafah ta jinjinawa Jamhuriyar Musulunci ta Iran kan yadda take ci gaba da yin turjuya domin kalubalantar bakar siyasar kasar Amurka musamman takunkumin da ta kakaba mata sakamakon kin mika wuya ga bakar siyasarta ta zalunci.