Kananan Yara Fiye Da 900 Ne Ake Tsare Da Su A Gidan Kurkukun H.K.Isra'ila
Kungiyoyin kasa da kasa da suke fafatukar kare hakkin al'ummar Palasdinu sun sanar da cewa: Tun daga farkon wannan shekara zuwa yanzu kananan yara fiye da 900 ake tsare da su a gidajen kurkukun haramtacciyar kasar Isra'ila.
Kungiyoyin kasa da kasar sun fitar da wannan sanarwa ce a ranar kananan yara ta duniya wato ranar 20 ga watan Nuwamban wannan shekara ta 2018, kamar yadda kungiyoyin suka yi kakkausar suka kan yadda mahukuntan gwamnatin Haramtacciyar kasar Isra'ila suke ci gaba da azabtar da kananan yara tare da tsare su a gidajen kurkuku.
Har ila yau kungiyoyin sun jaddada tsananin damuwarsu kan yadda sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila suke kai farmaki kan gidajen Palasdinawa tare da yin awungaba da kananan yara.