Hamas: Za'a Ci Gaba Da Zanga-Zangar Komawa Gida Har Zuwa Karshen Mamaya
Kungiyar Hamsa wacce take gwagwarmaya da HKI da makamai ta bayyana cewa Palasdinawa zasu ci gaba da zanga-zanga mai suna zanga-zangar dawowa gida a ko wace ranar Jumma'a har zuwa lokacinda za'a kawo karshen mamayar da HKI takewa Palasdinu.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Mahmood Al-Zahar daya daga cikin wadanda suka kafa kungiyar ta Hamsa sannan daya daga cikin shuwagabanninta yana fadar haka a jiya Lahadi . Al-Zahar ya kuma kara da cewa zanga-zangar dawowa gida wanda Palasdinawa suka fara tun watan Maris na wannan shekara ya samar da sakamako mai kyau ya zuwa yanzu.
Sannan ya kara da cewa za'a ci gaba da ita har zuwa karshen mamayar da HKI takewa al-ummar Palasdinu.
Ya zuwa yanzu Palasdinawa 220 ne suka yi shahada sannan wasu dubu 20 kuma suka ji rauni sanadiyyar zanga -zangar.