Jami'an Tsaro A Kasar saudiya Sun Kashe Mutane 5 A Yankin Watif
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i34718-jami'an_tsaro_a_kasar_saudiya_sun_kashe_mutane_5_a_yankin_watif
Mutane akalla 5 ne suka rasa rayukansu a kauyen Umm Al-Hamam na yakin Qatif a kasar Saudiya a lokacinda jami'an tsaron kasar suka kai sumame a kan mutanen kauyen.
(last modified 2019-01-08T03:22:46+00:00 )
Jan 08, 2019 03:22 UTC
  • Jami'an Tsaro A Kasar saudiya Sun Kashe Mutane 5 A Yankin Watif

Mutane akalla 5 ne suka rasa rayukansu a kauyen Umm Al-Hamam na yakin Qatif a kasar Saudiya a lokacinda jami'an tsaron kasar suka kai sumame a kan mutanen kauyen.

Tashar Talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa jami'an tsaron kasar Saudiya sun kai sumame a kauyen Umm Al-Hamam na yankin Qatif ne a jiya Litinin, sannan sun kwashe sa'o'i 15 suna kawanya da kauyen. A lkacin ne suka yi ta kwasar kayakin mutanen kauyen a matsayin ganimar yaki. Mazauna yankin Qtif na kasar Saudiyya dai mabiya mazhabar Shi'a ne, kuma sun dade suna kokawa kan irin wariyar da ake nuna masu a gwamnatin masarautar Ali Sa'ud.