An Zartar Da Hukuncin Kisa A Kan Jagoran Kungiyar Jihad Islami A Bangaladesh
https://parstoday.ir/ha/news/world-i19426-an_zartar_da_hukuncin_kisa_a_kan_jagoran_kungiyar_jihad_islami_a_bangaladesh
An zartar da hukuncin kisa a kan jagoran kungiyar Jihad Islami a kasar Bangaladesh bisa zargin bude wa tsohon jakadan Birtaniya a kasar wuta.
(last modified 2019-08-10T10:24:46+00:00 )
Apr 14, 2017 10:49 UTC
  • An Zartar Da Hukuncin Kisa A Kan Jagoran Kungiyar Jihad Islami A Bangaladesh

An zartar da hukuncin kisa a kan jagoran kungiyar Jihad Islami a kasar Bangaladesh bisa zargin bude wa tsohon jakadan Birtaniya a kasar wuta.

Tashar alalam ta bayar da rahoton cewa, ministan cikin gida na kasar Bangaladesh Asadu Zaman Khan ya sanar da cewa, an zartar da hukuncin kisa a kan Mufti Abdulhanan, jagoran kungiyar Jihad Islami, tare da wasu mutane biyu na hannun damarsa, bisa samunsu da hannu a harbin da aka yi wa tsohon jakadan Birtaniya a kasar Bangaladesh.

Tun kimanin shekaru 12 da suka gabata ne dai ‘yan kungiyar ta Jihad Islami suka budewa tsohon jakadan Birtaniya a kasar Bangaladesh wuta, amma ba su samu damar kashe shi ba, sai dai jami’an ‘yan sanda 3 sun rasa rayukansu,yayin da wasu mutane 79 suka samu raunuka.

Tun a cikin shekara ta 2014 ne dai wata kotu ta yanke hukuncin kisa a kan Mufti Abdulhannan tare da wasu na hannun damarsa, tare da yanke hukuncin daurin rai da rai a kan wasu 6 daga cikinsu.