Korea Ta Arewa Ta Yi Gwajin Sabon Makami Mai Linzami Da Safiyar Yau Lahadi.
https://parstoday.ir/ha/news/world-i19462-korea_ta_arewa_ta_yi_gwajin_sabon_makami_mai_linzami_da_safiyar_yau_lahadi.
Da safiyar lahadi ne dai Korea Ta Arewa ta gudanar da gwajin makami mai linzamin da ya tarwatse jim kadan bayan tahsinsa.
(last modified 2018-08-22T06:59:58+00:00 )
Apr 16, 2017 04:47 UTC
  • Korea Ta Arewa Ta Yi Gwajin Sabon Makami Mai Linzami Da Safiyar Yau Lahadi.

Da safiyar lahadi ne dai Korea Ta Arewa ta gudanar da gwajin makami mai linzamin da ya tarwatse jim kadan bayan tahsinsa.

Gwajin makamin na Korea Ta Arewa ya zo ne sa'oi kadan gabanin ziyarar da mataimakin shugaban kasar Amurka, Mike Pence zai kai Korea ta Kudu.

Manufar ziyarar ta mataimakin shugaban kasar ta Amurka dai ita ce tattaunwa da mahukuntan Korea  ta Kudu akan korea ta arewa da shirinta na mamaki ma linzami da kuma na makamin Nukiliya.

Tuni dai Amurkan ta aike da jiragen ruwa na yaki masu harba makamai masu linzami zuwa yankin, abinda ya kara haddasa zaman dar-dar a yankin.

A jiya asabar Korea ta Arewa ta yi bikin baje sabbin makamai masu linzami da su ke isa wata nahiya, da kuma wasu makaman masu tarwatsa jiragen ruwa na yaki.

Gwamnatin kasar ta Korea ta arewa ta sha alwashin maida martani akan duk wani hari da Amurkan za ta kai mata.