'Yan Sandan Myanmar Sun Tarwatsa 'Yan Buda Da Suka Kai Hari Kan Musulmi
May 11, 2017 07:28 UTC
Jmi'an 'yan sandan kasar Myanmar sun yi amfani da karfi wajen tarwatsa daruruwan 'yan addinin Buda da suka kai hari a kan musulmi.
Shafin yada labarai na Radionz cewa, a daren jiya mabiya addinin buda sun kaddamar da farmaki a kan musulmi a yankin Rangon, amma jami'an tsaro sun tsarwatsa su ta hanyar yin harbi a cikin isaka.
Maharan dai sun kai farmaki ne a kan makarantu da kuma masalatan musulmi, suna masu nuna rashin amincewarsu da duk wani aiki na ibada da musulmi za su gudanar a yankinsu, har sai sun biya haraji.
Tags