Janar Baqeri: Iran Da Siriya Za Su Girmama Kudurin Tsagaita Wuta A Siriya, Amma Za a Ci Gaba Da Fada Da Ta'addanci
https://parstoday.ir/ha/news/world-i28579-janar_baqeri_iran_da_siriya_za_su_girmama_kudurin_tsagaita_wuta_a_siriya_amma_za_a_ci_gaba_da_fada_da_ta'addanci
Babban hafsan hafsoshin sojojin kasar Iran Manjo Janar Muhammad Baqeri ya bayyana cewar Iran da Siriya za su girmama kudurin tsagaita wuta a Siriya na wata guda da Kwamitin Tsaron MDD ya fitar, to amma za a ci gaba da fada da ta'addancin da suke yi a kasar musamman hare-haren a wajen birnin Damaskus da 'yan ta'adda suke rike da shi.
(last modified 2018-08-22T07:01:28+00:00 )
Feb 26, 2018 02:17 UTC
  • Janar Baqeri: Iran Da Siriya Za Su Girmama Kudurin Tsagaita Wuta A Siriya, Amma Za a Ci Gaba Da Fada Da Ta'addanci

Babban hafsan hafsoshin sojojin kasar Iran Manjo Janar Muhammad Baqeri ya bayyana cewar Iran da Siriya za su girmama kudurin tsagaita wuta a Siriya na wata guda da Kwamitin Tsaron MDD ya fitar, to amma za a ci gaba da fada da ta'addancin da suke yi a kasar musamman hare-haren a wajen birnin Damaskus da 'yan ta'adda suke rike da shi.

Janar Baqeri ya bayyana hakan ne a wata ganawa da yayi da manema labarai a yammacin jiya Lahadi inda ya ce:, "A wannan karon ma, kamar yadda ya faru a baya, wadanda ba sa son zaman lafiya da tsaron kasar Siriya sun shigo da maganar tsagaita wuta don karfafa 'yan ta'adda bayan da suka ga irin nasarorin da sojojin Siriya suke samu a kansu".

Babban hafsan hafsoshin sojojin na Iran ya ci gaba da cewa: Duk da haka za mu girmama wannan kudurin, kamar yadda ita ma gwamnatin Siriya za ta girmama hakan, to amma lalle ban da yankin Goutha da ke wajen birnin Damaskus da 'yan ta'adda suke rike da shi", yana mai cewa za a ci gaba da kai wa 'yan ta'addan hari har sai an kawar da su .

Shugaban kasar Rasha ma Vladimir Putin ya shaida wa takwarorinsa na Faransa da Jamus cewa kudurin tsagaita wutan ba zai shafi fadar da ake yi da kungiyoyin 'yan  ta'adda a Siriyan ba wanda kasar Rashan take taka gagarumar rawa a cikinsa.

A shekaran jiya Asabar ce Kwamitin Tsaron MDD ya fitar da wani kuduri da ya bukaci a tsagaita wuta na kwanaki 30 a duk fadin kasar Siriya don abin da ya kira ba da damar kai agaji na gaggawa ga mabukata.