Kokarin Amurka Na Fitar Da Saudiyya Daga Cikin Kangin Tsaka Mai Wuya Da Ta Shiga A Yamen
https://parstoday.ir/ha/news/world-i33873-kokarin_amurka_na_fitar_da_saudiyya_daga_cikin_kangin_tsaka_mai_wuya_da_ta_shiga_a_yamen
Sakamakon matakan matsin lamba da kasashen Amurka da Saudiyya suke fuskanta tun bayan kisan gillar da aka yi wa dan jaridar Saudiyya mai adawa da masarautar kasar ta Saudiyya Jamal Khashoggi, mahukuntan Amurka suka fara batun neman hanyar warware rikicin kasar Yamen.
(last modified 2018-11-18T05:33:40+00:00 )
Nov 01, 2018 01:53 UTC
  • Kokarin Amurka Na Fitar Da Saudiyya Daga Cikin Kangin Tsaka Mai Wuya Da Ta Shiga A Yamen

Sakamakon matakan matsin lamba da kasashen Amurka da Saudiyya suke fuskanta tun bayan kisan gillar da aka yi wa dan jaridar Saudiyya mai adawa da masarautar kasar ta Saudiyya Jamal Khashoggi, mahukuntan Amurka suka fara batun neman hanyar warware rikicin kasar Yamen.

Sakataren harkokin wajen kasar Amurka Mike Pompeo ya bukaci dakatar da bude wuta a kasar Yamen yana mai jaddada yin kira ga rundunar kawance masarautar Saudiyya kan daukan matakan nisantar kaddamar da hare-hare kan yankunan da suke dauke da jama'a a kasar ta Yamen tare da gabatar da kira ga kungiyar Ansarullahi ta mabiya Huthi a kasar ta Yamen kan dakatar da kai hare-hare da makamai masu linzami kan kasar Saudiyya da nufin ganin an fara gudanar da zaman tattaunawa a tsakanin bangarorin biyu. 

Har ila yau sakataren tsaron kasar Amurka James Mattis shi ma ya bukaci kawo karshen yaki a kasar Yamen yana mai bayyana cewa: Dole ne a fara gudanar da zaman tattaunawa tsakanin bangarorin da suke yaki a kasar ta Yamen da nufin kai wa ga matakin sulhu.

A fili yake cewa: Mahukuntan Amurka ne suka bai wa masarautar Saudiyya damar kaddamar da hare-haren wuce gona da iri kan kasar Yamen, kuma bayan da yakin ya fi karfin Saudiyya ta dauki matakin kafa rundunar kawance domin murkushe al'ummar Yamen amma cikin 'yardan Allah a tsawon watanni 44 da ta kwashe tana kaddamar da hare-haren soji kan Yamen ta kasa cimma bakar aniyarta kan kasar.

Tabbas kaddamar da hare-haren wuce gona da iri kan kasar ta Yamen sun wurga al'ummar kasar cikin mummunan yana yi musamman kashe fararen hula da suka hada da mata da kananan yara gami da tsofaffi baya ga rusa duk wani abu mai amfani a kasar lamarin da ya tilastawa miliyoyin mutane yin gudun hijira gami da bullar cututtuka a tsakanin al'ummar kasar sakamakon amfani da makamai masu guba kansu.

Matakin da duniya ta dauka na taso kasar Saudiyya gaba sakamakon kisar gillar da ta yi wa Jamal Khashoggi shahararren dan jaridar kasar mai adawa da manufofin yarima mai jiran gado Muhammad bin Salman, mahukuntan Amurka suka bullo da dabarar rage zafi kan saudiyya ta hanyar kubutar da ita daga kangin manyan laifuffukan da take tafkawa a duniya musamman laifukan yaki a kasar Yamen.

Tuni dama al'ummar Yamen ta sanar da shirinta na amincewa da matakin gudanar da zaman tattaunawa da nufin kawo karshen matakan wuce gona da iri da ake dauka kan kasarta karkashin jagorancin masarautar Saudiyya, kamar yadda mahukuntan kasar ta Yamen suke ci gaba da jaddada rashin amincewarsu da duk wani matakin raba kasar ta hanyar bai wa wani yanki 'yancin cin gashin kai.