Venezuela : Kwamitin Tsaro Zai Kada Kuri'a Kan Kudurorin Rasha Da Amurka
A wani lokaci yau Alhamis ce, ake sa ran kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya, zai yi wani zaman kada kuri'a kan wasu kudurorin doka masu sabani da juna da kasashen Amurka da Rasha suka gamatar masa kan batun Venezuela.
A kudirin da Amurka ta gabatar, ta yi kira da a gudanar da zaben shugaban kasa, mai gaskia cikn adalci da haske da kuma shigar da kayan agaji ba tare da wata matsala ba a kasar ta Venezuela.
A kudirin da ta gabatar kuwa Rasha, ta nanata bukatar ganin an dama da gwamnatin Shugaba Nicolas Maduro, nada rawar da zata taka wajen wajen warware rikicin kasar, tare da kira ga kasashen duniya dasu tsame hanayensu a cikin rikicin siyasar kasar ta Venezuella.
Dama tun farkon rikicin kasashen Rasha da China, sun yi allawadai da tsoma bakin kasashen yamma a rikicin cikin gida na kasar ta Venezuela, dake fama da matsalar tattalin arziki.
Rasha dai na ganin kokarin Amurka na shigar da kayan agaji a Venezuela, wani yunkuri ne na kifar da gwmanatin Shugaba Nicolas Maduro.