-
Harin Paris : Saleh-Abdesalam Yaki Cewa Ufan Gaban Alkalai
May 20, 2016 06:05karon farko daya bayyana gaban kotu akan tuhumar da ake masa da shirya harin 13 ga watan Nowamba a Paris, Saleh-Abdesalam yaki amsa tambayoyin alkalai.
-
An Gano Tarkacen Jirgin EgyptAir
May 20, 2016 05:08Rundinar sojin kasar ta sanar da gano takarcen jirgin saman EgyptAir wanda ya fada a tekun Bahar Rum da jijibin safiyar Alhamis.
-
Kasar Amurka Ta Goyi Bayan Ci Gaba Da Kasancewar Iraki A Matsayin Kasa Daya Dunkulalliya
May 19, 2016 23:40Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Amurka ya bayyana cewa: Gwamnatin Amurka tana goyon bayan ci gaba da kasancewar Iraki a matsayin kasa daya dunkulalliya, don haka ba ta amince da duk wani shirin ballewar wani yanki daga cikin kasar ta Iraki ba.
-
Magoya Bayan Shugabar Kasar Brazil Sun Ce Dakatar Da Ita Juyin Mulki Ne A Kasar
May 19, 2016 22:51Shugabar kasar Brazil Dilma Rousseff da aka dakatar da ita daga kan shugabancin kasar Brazil domin fuskantar shari'a ta ce an yi hakan ne domin biyan bukatun wasu manyan kasashen duniya.
-
Jirgin Egypt Air Ya Fadi Ne A Tekun Bahar Rum
May 19, 2016 06:41Rahotanni dake cin karo da juna na cewa jirgin fasinja nan na Egypt Air daya taso daga Paris zuwa Alkahira ya fadi ne a tekun Bahar Rum.
-
Wani Jirgin Saman Fasinjan Kasar Masar Ya Bace A yau Alhamis
May 19, 2016 00:56Kamfanin jiragen samar kasar Masar (Egypt Air) ya sanar da bacewar wani jirgin saman fasinjar da ke dauke da mutane 69 a cikinsa a kan hanyarsa ta zuwa birnin Alkahira, babban birnin kasar Masar din daga birnin Paris, babban birnin kasar Faransa.
-
Belgium Ta Yi Suka Kan Gina Katangar Tsaro Domin Hana 'Yan gudun Hijira Shiga Turai
May 18, 2016 09:55Ministan harkokin wajen kasar Belgium ya ce: Gina katangar tsaro da nufin hana kutsen 'yan gudun hijira zuwa cikin kasashen yammacin Turai ba zai taba magance matsalar ba.
-
Ayatullahi Makarim Shirazi Ya Jaddada Wajabcin Samun Hadin Kai Tsakanin Shi'a Da Sunnah
May 18, 2016 09:53Daya daga cikin manyan malaman mazhabar shi'a da ake komawa gare su domin sanin hukunce-hukuncen shari'a a duniya da ke birnin Qum na kasar Iran ya jaddada wajabcin samun hadin kai da taimakekkeniya tsakanin shi'a da sunnah.
-
Rasha Ta Ce; Sojojin Siriya Sune Mafi Karfin Runduna A Fagen Yaki Da Ta'addanci A Kasar
May 18, 2016 09:52Ministan harkokin wajen kasar Rasha ya bayyana cewa: Sojojin Siriya sune mafi karfin rundunar soji da zata iya kawo karshen ayyukan ta'addanci a kasarsu.
-
Kokarin Ganin An Kawo Karshe Azabtar Da Mutanen Da Ake Tsare Da Su A Kasar Tunusiya
May 18, 2016 09:52Ministan kula da harkokin kare hakkin bil-Adama a kasar Tunusiya ya bayyana fatan ganin an kawo karshen azabtar da mutanen da ake tsare da su a cibiyoyin tsaron kasar.