-
Sojojin Siriya Sun Fatattakin 'Yan Ta'addan Da'esh Daga Palmyra Na Siriya
Dec 11, 2016 07:49Rahotanni daga kasar Siriya sun bayyana cewar sojojin Siriya da suke samun daukin jiragen yakin kasar Rasha sun fatattaki 'yan kungiyar ta'addancin nan ta Da'esh da suka yi kokarin sake kwace garin Palmyra mai tsohon tarihi daga hannun dakarun Siriyan a jiya.
-
Kimanin Kashi 82 Cikin Dari Na Amurkawa Sun Yarda Cewa Ana Kuntata Wa Musulmi
Dec 10, 2016 15:28Sakamakon wani jin ra'ayin jama'a da aka gudanar a kasar Amurka ya yi nuni da cewa kimanin kashi 82% na Amurka sun yi amannar cewa ana kuntata wa musulmi a kasar.
-
Wani Sabon Rikici Ya Tarwatsa Mutane 13,000 Daga Muhallinsu A Jamhuriyar DR Congo
Dec 10, 2016 02:23Majalisar Dinkin Duniya ta sanar da cewa: Bullar wani sabon dauki ba dadi tsakanin sojojin gwamnatin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo da 'yan tawayen kasar ya tilastawa mutane kimanin 13,000 gudun hijira daga muhallinsu.
-
Kasashen Amurka Da Birtaniyya Na Leken Asirin Shugabannin Afirka
Dec 09, 2016 03:07Jaridar Le Monde ta kasar Faransa ta buga wani labari da ke cewa tana dauke da wasu takardun shaida da ke nuni da cewa Ma'aikatun Leken Asirin Amurka da na Birtaniya suna gudanar da leken asiri kan shugabanni da manyan 'yan kasuwar 20 na Afirka.
-
'Yan Kungiyoyin Fararen Hular Bahrain Sun Yi Gangami A Gaban Otel Din Trump a Birnin Washington
Dec 08, 2016 14:43Yan kungiyoyin farar hular Bahrain sun taro gaban Otel din Donald Trump zababben shugaban Amurka a birnin Washington
-
Barak Obama Ya Yi Furuci Da Rashin Yiyuwar Murkushe 'Yan Kungiyar Taliban A Afganistan
Dec 08, 2016 02:17Shugaban kasar Amurka ya yi furuci da cewa: Sojojin Amurka ba zasu iya murkushe 'yan ta'addan kungiyar Taliban da ke kasar Afganistan ba.
-
Sojin Syria Sun Kwace Tsohon Birnin Halab (Aleppo) Daga Hannun 'Yan Ta'adda
Dec 07, 2016 13:37Sojojin kasar Syria sun kwace yanki na karshe da 'yan tawayen kasar ke rike da shi a tsohon birnin Halab (Aleppo) a ci gaba da shirin da sojojin suke da shi na fatattakan 'yan ta'addan daga arewacin garin na Halab da suke rike da shi tsawon shekaru.
-
Mutanen New York Na Ci Gaba Da Nuna Rashin Amincewa Da Zaman Trump A Garin
Dec 07, 2016 13:37Rahotanni daga birnin New York na Amurka na nuni da cewa dubun dubatan mutanen garin ne suka sanya hannu kan wata takarda don nuna rashin amincewarsu da ci gaba da zaman shugaban Amurka mai jiran gado Donald Trump a garin saboda irin kudin da ake kashewa wajen tsaronsa.
-
Sama Da Mutane 40 Sun Mutu A Hatsarin Jirgi A Kasar Pakistan
Dec 07, 2016 13:37Rahotanni daga kasar Pakistan sun ce alal akalla mutane 40 sun rasa rayukansu sakamakon faduwar da wani jirgin sama mallakar kamfanin Pakistan International Airlines (PIA) yayi a yau din nan Laraba a Arewacin kasar ta Pakistan.
-
Waziyar Kasar Jamus Ta Bukaci A Hana Mata Musulmi Sanye Burka Mai Rufe Fuska
Dec 07, 2016 02:13Waziyar kasar Jamus Angela Merkel ta bukaci a hana mata musulmi sanya burka mai rufe fuska a kasar,