Duniya
-
Duniya Na Tir Da Mallaka Wa Yahudawan Mamaya Tuddan Golan
Mar 26, 2019 03:23Kasashen duniya sun fara maida martani kan matakin shugaba Donald Trump na Amurka, na amincewa da tuddan golan a mastayin wani yanki na mahukuntan yahudawan mamaya na Isra'ila.
-
New Zeland : Musulmi Sun Koma Ibada A Masallacin Christchurch
Mar 23, 2019 06:00Musulmi a New Zeland, sun koma ibada a babban masallacin Christchurch, karon farko bayan mummunan harin ta'addancin da aka kai kan musulmin a ranar 15 ga watan Maris din nan.
-
Iran : Zarif Na Halartar Taron Gaggawa Na OIC Kan Kisan Gillan New Zealand
Mar 22, 2019 07:33A yammacin jiya Alhamis ne ministan harkokin wajen kasar Iran, Dakta Muhammad Jawad Zarif ya isa birnin Istanbul na kasar Turkiyya don halartar taron gaggawa na kungiyar hadin kan kasashen musulmi OIC da nufin tattauna harin ta'addancin da aka kai wa masallata a wasu masallatai guda biyu na kasar New Zealand.
-
Tarayyar Turai Ta Ki Yarda Da Tabbatar Da Ikon 'Isra'ila' A Kan Tuddan Golan Na Siriya
Mar 22, 2019 07:30A wani abu da ake ganinsa a matsayin fito na fito da Amurka, kungiyar Tarayyar Turai ta sanar da rashin amincewarta da tabbatar da ikon haramtacciyar kasar Isra'ila a kan tuddan Golan na kasar Siriya.
-
Guteress Ya Taya Al'ummar Iran Murnar Noruz
Mar 21, 2019 09:53Saktare Janar na Majalisar Dinkin Duniya ya taya al'ummar kasashen dake bikin Noruz murna
-
Faransa Ta Nuna Adawarta Da Dage Ficewar Birtaniya Daga Cikin Kungiyar Tarayyar Turai
Mar 21, 2019 09:51Faransar ta ce ba za ta amince da bukatar Birtaniyar ba har sai ta samu tabbacin cewa 'yan majalisar kasar Birtaniyar za su amince da ficewar Birtaniyar daga cikin kungiyar Tarayyar Turai.
-
An Sake Dage Zaben Shugaban Kasa A Afganistan
Mar 21, 2019 05:54Hukumar zabe mai zaman kanta a Afganistan ta sanar da dage zaben shugaban kasar zuwa ranar 28 ga watan Satumba na wannan shekara ta 2019.
-
Faransa : Za'a Jibge Sojoji Don Tunkarar Masu Bore
Mar 20, 2019 14:43Hukumomi a Faransa, sun ce za'a tsaurara matakan tsaro ta hanyar jibge sojoji na tawagar yaki da ta'addanci domin tunkarar masu zanga zanga da akewa lakabi da masu ''dorawa riga'' a ranar Asabar mai zuwa.
-
China ta Kame Musulmi Kimanin Dubu 13 Da Yaki Da Ta'addanci
Mar 20, 2019 08:54Gwamnatin kasar China ta sanar da kame wadanda ta kira 'yan ta'adda kimanin dubu 13 a yankunan musulmin kasar.
-
MDD Ta Yi Alkawarin Daukar Matakan Takaita Barazanar Tashin Hankali A DRC
Mar 20, 2019 05:55Majalsiar Dinkin Duniya, ta yi alkawarin daukar matakan da suka dace na takaita barazanar tashin hankali a Jamhuriya Demokuradiyyar Congo.