Mar 21, 2019 05:54 UTC
  • An Sake Dage Zaben Shugaban Kasa A Afganistan

Hukumar zabe mai zaman kanta a Afganistan ta sanar da dage zaben shugaban kasar zuwa ranar 28 ga watan Satumba na wannan shekara ta 2019.

A cikin sanarwar data fitar hukumar zaben kasar ta (CEI), ta ce an dage zaben ne duba da mastalolin da aka fuskanta a zaben 'yan majalisar dokokin kasar na watan Oktoban shekara data gabata.

Don hana ne a cewar hukumar ana bukatar lokaci na shiri don tunkarar zaben shugaban kasar yadda ya kamata da kuma bda dama ga mutane su yi rejista.

Saidai hukumar ta ce zaben zai gudana kamar yadda aka tsara idan dukkan bangarorin da zaben ya shafa da kuma gwamnatin kasar da kasashen duniya suka bata kudaden da take bukata don shirya zaben.

Wannan ba shi ne karo na farko ba da aka dage zaben da aka shirya yi a ranar 20 ga watan Afrilu mai zuwa.