Mar 26, 2019 03:43 UTC
  • Nijar : Mutum 14 Boko Haram Ta Kashe A Diffa

Rahotanni daga Jamhuriya Nijar na cewa fararen hula a kalla 14 ne aka kashe tare da sace wasu mata 2, ranar Asabar da daddare, a wani jerin hare-hare da kungiyar Boko Haram ta kai wasu kauyuka 3 na yankin Gueskerou dake jihar Diffa a kudu maso gabashin kasar, kusa da iyakar kasar da Nijeriya.

An tabbatar da aukuwar hare-haren ne a shafin sada zumunta na sabon gwamnan shiyyar Diffa, Mohammed Mouddour, wanda ya je yankin domin ganin illar da hare-haren suka haifar, da kuma mika jajen gwamnatin kasar ga wadanda al'amarin ya shafa.

Gwamnan ya ce, 'yan kungiyar ta'adda na amfani ne da janyewar kogin Yobe wajen dawowa da kai hare-hare a baya bayan, inda suke tsallakawa daga iyakar Najeriya su kai hari kan fararen hula.

Gwamnan ya sanar da cewa, an dauki kwararen matakan kare aukuwar irin wadannan hare-hare ta hanyar tura jami'an tsaro yankunan.

Tags