Mar 26, 2019 03:39 UTC
  • Ambaliyar Ruwan Sama A Iran

A Iran, ana ci gaba da kai dauki ga mutane dama yankunan da ambaliyar ruwa ta shafa a kwanan nan.

Daruruwan mutane ne aka rawaito cewa ambaliyar ruwan ta shafa a yankuna takwas na kasar.

Yau kusan kwanaki shida kenan da masu aikin cewa gami da sojoji ke gudanar da ayyukan ceto a wani gangami da akayi wa lakabi da ceto mutane 56,000 da ambaliyar ruwan ta shafa musamman a cikin kauyuka, sakamakon ruwan sama da tabkawa kwanan nan ba kakkautawa.

Ambaliyar ta fi shafar yankuna biyu dake arewacin kasar, da suka hada da Golestan da kuma Mazandaran. 

A jiya Litini kuma ruwan sama a wasu yankunan kasar da ba'a saba ganin irinsu ba, sun shafi yankunan Lorestan, Fars, Kohguilouyeh da kuma Boyer Ahmad.

A yankin Chiraz dai an rawaito rasa rayuka na mutum 18 da kuma wasu 94 da suka raunana a ambaliyar ruwan kamar yadda gidan talabijin na #PRESSTV ya rawaito.

A halin da ake ciki hukumar hasashen yanayi ta kasar, ta yi matsakaicin gargadi akan ruwan sama da za'a samu a cikin wkanaki uku masu zuwa a cikin yankunan 12 na kasar da suka hada da Fars, Ispahan, Kurdistan da Qom.

 

Tags