Mar 26, 2019 03:23 UTC
  • Duniya Na Tir Da Mallaka Wa Yahudawan Mamaya Tuddan Golan

Kasashen duniya sun fara maida martani kan matakin shugaba Donald Trump na Amurka, na amincewa da tuddan golan a mastayin wani yanki na mahukuntan yahudawan mamaya na Isra'ila.

A Jiya ne Trump, ya sanya hannu kan sabon kudirin, wanda tuni daka fara dangantasa da sabawa dokokin kasa da kasa da kuma keta hurimin kasar Siriya.

Da take maida martaki kan matakin, ma'aikatar harkokin wajen Siriya, ta ce hakan sabawa hurimin kasar ne, hasali ma Trump baida iko da hurimin da zai yanke wannan matsayi.

Kuma a cewar Siriya wannan goyan bayan da mahukuntan Washigton suka baiwa Isra'ila, ya sanya ta zama abokiyar gaba ta farko ga kasashen Larabawa.

A cewar ministan harkokin wajen Siriyar Walid Moallem, matakin na Donald Trump, zai kara ware Amurka a duniya.

Ko baya ga Siriya, akwai kasashe makobtanta da dama da suka yir tir da matakin, inda ma'aikatar harkokin waje ta Labanon ta ce ''Golan'' yanki ne na Larabawan Siriya, kuma babu wani abu da zai iya sauya shi.

Ita a nata bangare Iraki ta nuna matukar goyan bayanta ga dokokin kasa da kasa kan batun yankin na Golan, tare da bukatar kawo karshen mamayar da Isra'ila le wa tuddan.

A cewar kasar Jodan kuwa, ''Golan'' kasa ce dake karkashin mamaya, kuma Isra'ila ba zata iya  mamaye ta ba.

Ita kuwa Turkiyya ta ce matakin na Trump, kyauta ce ta kuri'a da aka baiwa fira ministan Isra'ilar Benjamin Netanyahu.

Tags