New Zeland : Musulmi Sun Koma Ibada A Masallacin Christchurch
Musulmi a New Zeland, sun koma ibada a babban masallacin Christchurch, karon farko bayan mummunan harin ta'addancin da aka kai kan musulmin a ranar 15 ga watan Maris din nan.
Tagwayen hare haren bindigan wanda wani mai sassauran ra'ayi dan asalin kasar Austria ya kai a waccen Jum'ar data gabata ya yi sanadin shahadar musulmi 50.
Bayan hakan ne 'yan sandan yankin suka rufe masallacin domin gudanar da bincike da kuma tabbatar da tsaro.
'Yan sanda a kasar sun ce an kuma gudanar da gyara a gudan masallacin na biyu na Linwood, inda dan ta'addan ya kashe mutane, saidai basu bayyana takamaimai ranar da za'a fara ibada a masallacin ba.
Saidai sun ce za'a karfafa matakan tsaro, ta hanyar jibge 'yan sanda a masallatan guda biyu, har sai abunda hali ya yi.