Mar 20, 2019 14:30 UTC
  • Hare Haren Amurka A Somaliya, Laifukan Yaki Ne_ Amnesty

Kungiyar kare hakkin bil adama ta kasa da kasa, Amesty International, ta ce hare haren da Amurka ke kaiwa a Somaliya zasu iya kasancewa laifukan yaki.

A rahoton data fitar kungiyar ta ce, hare haren da Amurka ke kaiwa kan mayakan Al'shabab sun karu matuka a shekarun baya bayan nan, inda harma suke shafar fararen hula, wanda kuma hakan zai iya kasancewa aikata laifukan yaki.

Alkalumman da kungiyar ta AMnesty, ta fitar sun ce, sama da hare hare 100 ne jiragen Amurka na yaki ko marar matuki suka kai tun daga watan Afrilu na shekara 2017, wanda kuma hakan ya zarta hare haren da Amurkar ta kai a kasashen Libiya da Yemen gabadaya.

Hare haren a cewar rahoton sun wuce gona da iri, sannan sun keta dokokin kasa da kasa, wanda hakan kuma tamakar aikata laifukan yaki ne, kamar yadda rahoton wanda aka wa taken '' yakin boye na Amurka A Somaliya''.

Rahoton dai ya ta'allaka ne kan bayanai da kungiyar ta samu daga hotunan tauraren dan adam, da kuma tarkacen boma boman da aka tattara a wuraren, da bayanai daga makusanta wadanda hare haren sukayi ajalinsu.

Saidai duk da gabatar mata da wannan rahoton, Amurka ta bakin rundinarta ta AFRICOM a Afrika, ta musunta kashe fararen hula, a yakin data ce tana yi ne kan mayakan Al'shabab.

Tags