Mar 14, 2019 16:58 UTC
  • Iran Ta Mayar Da Martani Kan Rahoton Amurka Na Kare Hakkin Bil Adama

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Iran Bahram Qasemi ya mayar da martani kan rahoton Amurka na shekara-shekara kan kare hakkokin bil adama a kasashen duniya.

 A lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai yau a birnin Tehran, Bahram Qasemi ya bayyana cewa, gwamnatin Amurka ba ta da hurumin da za ta yi magana a kan batun kare hakkin bil adama a kasashen duniya, a daidai lokacin da ake kasarta ake take hakkokin 'yan adam da nuna musu wariya saboda addininsu ko kuma launin fatarsu.

Ya ce batun rahoton kare hakkin bil adama na Amurka magana ce ta siyasa, domin kuwa kasashen da suka suna wajen cin zarafin dan da keta huruminsa da yi masa kisan kiyashi, ba sa daga cikin masu keta hakkokin 'yan a wajen Amurka, saboda suna dasawa da ita, inda ya buga misali da Isra'ila da kuma kasashen larabawa masu kisan mata da kananan yara a Yemen.

Amma  kuma a daya bangaren duk wata kasa da take kare hakkokin 'yan kasarta, matukar ba ta dasawa da Amurka,a  wurin Amurka tana cikin masu take hakkin 'yan adam.

Ya ce saka Iran a cikin rahoton an Amurka ba abin mamaki ba ne, wata kila da Amurka ba ta saka Iran ba a cikin rahoton nata, to da shi ne abin mamaki.

Tags