Mar 21, 2019 15:51 UTC
  • Jagora : Noruz 1398, Shekara Ce Mai Cike Da Damarmaki

Yau Alhamis wacce tayi daidai da 21 ga watan Maris 2019, akan shiga sabuwar shekara hijira shamsiyya ta 1398.

A sakon da ya gabatar na murnar shiga sabuwar shekarar, jagoran juyin juya halin musulinci na Iran, Ayatollah Seyyed Ali Khamenei, ya bayyana cewa wannan sabuwar shekara, da yardar Allah zata kasance shekara mai cike da damarmaki, ba wai barazana ba.

Jagoran ya bayyana hakan ne a yayin da yake gabatar da jawabinsa na sabuwar shekara kamar yadda yake a al'ada, tun daga hubbaren Imam Reza (AS), dake birnin Mashhad a arewa maso gabashin kasar ta Iran.

A yayin jawabin nasa, Ayatollah Sayyid Ali Khamenei, ya taya dukkan bangarorin al'umma na Iran da kasashen makobtanta murnar shiga sabuwar shekarar.

Jagoran ya kuma tabo batutuwa da dama na cikin gida dana yankin da kuma na kasa da kasa.

A lokacin da ya tabo batun matsin lamba da barazana ta makiya, jagoran ya ce takunkuman zaluncin da aka kakaba wa Iran, sun kasance wata dama da kuma kasancewa tamakar jarabawa,wacce zata baiwa kasar ta Iran, damar tunkarar duk wasu irin matsaloli na tafiyar da kasar, da kuma kaucewa duk wani yunkuri na mamaya daga kasashen ketare.

Jagoran ya kuma kara jadadda cewa har kulun, Jamhuriya Musulinci ta Iran, zata ci gaba da karfafa matakan kare kanta, duk da barazanar da manyan kasashen duniya ke yi mata.

http://ha.hausatv.com/

Tags