Iran : Rohani Ya Samu Kyakyawan Tarbe Ga Dukkan Bangarori A Iraki
(last modified Wed, 13 Mar 2019 05:29:48 GMT )
Mar 13, 2019 05:29 UTC
  • Iran : Rohani Ya Samu Kyakyawan Tarbe Ga Dukkan Bangarori A Iraki

Yau kwana na uku kuma na karshe kenan da shugaban kasar Iran, Dakta Hassan Rohani, ke gudanar da ziyarar aiki a kasar Iraki.

A yayin ziyarar tasa shugaba Ruhani ya gana da dukkan bangarorin jami’an kasar ta Iraki.

Daga cikin manyan jami’an Irakin da shugaban Ruhani ya gana dasu, akwai  fira ministan kasar, Adel Abdel Mahdi, da kuma shugaban kasar Barham Saleh da kuma Ayatollah Ali Sistani, da dai saurensu.

Haka zalika kasashen biyu sun tattauna kan batutuwa da dama da suka shafi alaka a tsakaninsu da suka da tattalin arziki kasuwanci, tsaro da dai saurensu.

Sabanin ziyarar da shugaban kasar Amurka  Donald Trump ya kai a watan Disamba cikin dare a boye ba tare da ma sanin mahukuntan kasar Irakin ba, wanda aka danganta da keta hurumin kasar, shugaba Ruhani na Iran ya samu kyaukyawan tarbe daga bangarori daban daban na Irakin da kuma mahukuntanta.

Iran ita ce kasa ta biyu wajen huldar kasuwanci da Iraki, bayan Turkiyya, inda kasashen biyu ke son fadada kasuwancinsu zuwa dala Biliyan ashirin a ko wacce shekara.