Mar 21, 2019 09:58 UTC
  • Mayakan Boko Haram Sun Kashe Mutune 4 A Najeriya

Kimanin mutune 4 ne suka rasa rayukansu sanadiyar harin ta'addanci na kungiyar boko haram a Najeriya

Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya habarta cewa wasu mahara da ake kyautata zaton 'yan kungiyar boko haram ne sun kai hari a wani kauye na jihar Borno dake shiyar arewa maso gabashin Najeriya, inda suka yiwa wasu manoma hudu kissan gilla.

A wani hari mai kama da  wannan, mayakan na boko haram sun kashe mutum 3 a jihar Adamawa dake kan iyaka da jihar ta Borno ranar Talatar da ta gabata.

kungiyar ta Boko haram ta yi kaurin suna wajen kisan fararen hula musaman manoma da makiya a jihar ta Borno, inda suke zarkin makiyayen da manoman da baiwa jami'an tsaron kasar da 'yan kwato da gora rahoto game da ayyukansu.

Tun a shekarar 2009 ne kungiyar ta'addancin nan ta Boko haram ta fara kai hare-hare a yankunan arewa maso gabashin Najeriya, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane sama dubu 20 tare da hijrar sama da mutum miliyan biyu da dubu 600 bisa gidaddigar MDD, a shekarar 2013 kungiyar ta fadada kai hare-harenta zuwa kasashen Nijer, Kamaru da Tchadi.

Tags