Mar 19, 2019 14:50 UTC
  • Hukumar INEC Ta Dakatar Da Tattara Sakamakon Zaben Bauchi

Hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya INEC ta dakatar da tattara sakamakon zaben jihar Bauchi, daya daga cikin jihohi shida da tace zabensu na gwamna bai kammala.

Dakatar da tattara sakamakon zaben, ya biyo bayan wani zama da kotun tarayya tayi yau Talata, inda ta bayar da umarnin dakatar da tattara sakamakon zaben gwamnan jihar ta Bauchi.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake shirye-shiryen tattara sakamakon karshe na jihar, bayan da hukumar zabe a kasar ta bayyana zaben jihar a matsayin wanda bai kammala ba.

Kotun ta baiwa hukumar ta INEC, umarnin dakatar da tattara sakamakon zaben karamar hukumar Tafawa Balewa da ke Bauchi, bayan da jam'iyyar APC da Gwamnan jihar Mohammed Abubakar suka shigar da kara a gaban kotun, kamar yadda jaridar Daily Trust ta bayyana.

Tags