Mar 22, 2019 07:33 UTC
  • Iran : Zarif Na Halartar Taron Gaggawa Na OIC Kan Kisan Gillan New Zealand

A yammacin jiya Alhamis ne ministan harkokin wajen kasar Iran, Dakta Muhammad Jawad Zarif ya isa birnin Istanbul na kasar Turkiyya don halartar taron gaggawa na kungiyar hadin kan kasashen musulmi OIC da nufin tattauna harin ta'addancin da aka kai wa masallata a wasu masallatai guda biyu na kasar New Zealand.

A yau juma'a ne dai ake sa ran za a gudanar da taron karkashin jagorancin ministan harkokin wajen kasar Turkiyyan, Mevlut Cavusoglu don tattauna batun harin ta'addancin da wani dan ta'adda ya kai wasu masallatai guda biyu a garin Christchurch,  na kasar New Zealand din da yayi sanadiyyar mutuwar alal akalla masallata 49 da kuma wasu da dama da suka sami raunuka a ranar Juma'ar da ta gabata.

A wata sanar da ma'aikatar harkokin wajen Turkiyyan ta fitar, ta ce an gayyaci wasu wakilai daga cibiyoyin kasa da kasa da suka hada da na MDD, Tarayyar Turai da dai sauransu.

Taron dai ya biyo bayan wata tattaunawa ce da ta gudana tsakanin ministan harkokin wajen kasar Iran Dakta Muhammad Jawad Zarif da takwararsa na kasar Turkiyya Mevlut Cavusoglu a farko-farkon makon nan inda Dakta Zarif din ya bukaci da gudanar da taron na gaggawa don tattauna wannan danyen aikin.

 

Tags