Mar 20, 2019 05:55 UTC
  • MDD Ta Yi Alkawarin Daukar Matakan Takaita Barazanar Tashin Hankali A DRC

Majalsiar Dinkin Duniya, ta yi alkawarin daukar matakan da suka dace na takaita barazanar tashin hankali a Jamhuriya Demokuradiyyar Congo.

Da take sanar da hakan, babbar wakiliyar musamman ta MDD a jamhuriyar demokuradiyyar Congo, Leila Zerrougui, ta ce hukumar za ta yi dukkan abin da ya dace domin takaita barazanar barkewar tashin hankali a kasar.

Mme  Zerrougui, ta bayyna haken nelokacin da take karin haske ga kwamitin sulhun MDD game da halin da ake ciki a kasar.

Duk da cewar an dan samu zaman lafiya a lokacin gudanar da zaben kasar, Zerrougui ta fadawa kwamitin sulhun MDDr cewa, har yanzu, akwai damuwa game da yanayin ci gaba a yankunan gabashin kasar, inda kungiyoyin masu dauke da makamai ke ci gaba da cin karensu babu babbaka.

Domin shawo kan wannan matsalar, jami'ar ta ce, dakarun MONUSCO na bakutar gwamnati ta kara tura dakarunta domin kara musu karfi wajen cimma nasarar tabbatar da tsaro da kuma aikin sasanto da suke a tsakaninn al'ummomin yankunan kasar.