-
Benezuela : 'Yan Adawa Zasu Shirya Zaben Raba Gardama Don Tsige Shugaba Maduro
Mar 08, 2016 12:56'Yan adawa dake da rinjaye a majalisar dokokin Benezuela na nazarin bude wani shiri da zai ga gudanar da wani zaben jin ra'ayin al'umma kasar domin tsige shugaban kasar mai ci Nicolas Maduro.
-
UNHCR Ta Damu Dangane Da Yarjejeniyar da EU Ta Cimma Da Turkiya Kan 'Yan Gudun Hijira
Mar 08, 2016 11:25Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD ta nuna matukar damuwar ta dangane da yarjejeniyar wucin gadin da kungiyar tarraya Turai ta cimma da Turkiya kan 'yan gudun hijira.
-
Amurka Ta Sanar Da Hallaka 'Yan Ta'addan Al-Shabab 150 A Somaliya
Mar 08, 2016 02:14Rundunar sojin Amurka ta sanar da cewa ta samu nasarar hallaka sama da mayakan kungiyar 'yan ta'addan nan ta Al Shabab ta kasar Somaliya 150 a wani hari da suka kai musu da jirgin yaki mara matuki.
-
Gumurzu Tsakanin Jami'an Tsaron Tunusiya Da 'Yan Ta'adda Ya Lashe Rayukan Mutane 53
Mar 07, 2016 14:02Wasu gungun 'yan ta'adda sun farma garin Ben Gardane da ke gabashin kasar Tunusiya kusa da kan iyaka da kasar Libiya a safiyar yau Litinin, inda suka fuskanci mai da martani daga jami'an tsaron kasar.
-
Yiyuwar cimma matsaya tsakanin Turai da kasar Suizilland dangane da 'yan gudun hijra
Mar 06, 2016 11:08Ministan Harakokin wajen Suizilland ya sanar da cewa a kwai yiyuwar cimma matsaya tsakanin kasar sa da tarayyar Turai dangane yawan 'yan gudun hijrar da kasar za ta karba
-
Saudiyya Ta Ki Amincewa Da Kudurin Da Kwamitin Tsaron MDD Ya Fitar Kan Kasar Yamen
Mar 05, 2016 02:50Jakadan Saudiyya a Majalisar Dinkin Duniya ya yi suka kan sabon kudurin da kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya ya fitar kan matsalolin rayuwa da al'ummar Yamen suka shiga sakamakon hare-haren wuce gona da irin masarautar Saudiyya kan kasar.
-
Yan Gudun Hijira Kimanin 135,000 Ne Suka Samu Shiga Cikin Kasashen Turai A Wannan Shekara Ta 2016
Mar 05, 2016 02:50Hukumar Kula da 'Yan Gudun Hijira Ta Majalisar Dinkin Duniya ta sanar da cewa; Daga farkon wannan shekara ta 2016 zuwa wannan wata na Maris 'yan gudun hijira da yawansu ya kai 134,905 suka samu tsallakawa zuwa cikin kasashen Yammacin Turai.
-
Kasashen Rasha Da Aljeriya Sun Fara Tattaunawa Kan Samar Da Cibiyar Nukiliya A Kasar Ta Aljeriya
Mar 05, 2016 02:27Gwamnatin Aljeriya ta bayyana cewa zata yi kokarin samar da cibiyar makamashin nukiliya na zaman lafiya a kasar domin bunkasa ci gabanta ta hanyar bada kwangilar gina cibiyar ga kasar Rasha.
-
MDD Ta Sanar Da Karuwar Zarge Zargen Lalata Da Kananan Yara Tsakanin Dakatunta
Mar 04, 2016 13:01Majalisar Dinkin Duniya ta sanar da cewa an samu karuwar zarge zargen lalata da kananan yara da yin fyade wa mata da ake yi wa dakarun tabbatar da zaman lafiya na majalisar a shekarar da ta gabata ta 2015.
-
Rikicin yankin Darfur ya raba Mutane sama da million biyu da mahalinsu
Mar 04, 2016 00:39MDD da kungiyar AU sun bayyana cewa rikici tsakanin sojojin Sudan da 'yan tawaye ya yi sanadiyar raba mutane sama da million biyu da mahalinsu a yankin Darfur dake yammacin kasar