-
Wata Mota Ta Burma Cikin Jama'a A Birnin Manchester Na Kasar Britania
Apr 17, 2018 14:39Wata mota ta burma a cikin jama'a a birnin Manchester na kasar Britania a jiya litinin ya kuma yi sanadiyyar raunata mutane akalla 6.
-
Majalisar Dokokin Tarayyar Turai Ta Zama Wurin Allah Wadau Da Shugaban Kasar Faransa.
Apr 17, 2018 14:38A dai-dai lokacinda shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron yake jawabi a majalisar dokokin tarayyar Turai a birnin Strasbourg na gabacin kasar Faransa, kuma mazaunin majalisar tarayyar Turai a yau yan majalisar sun nuna rashin amincewarsu da shishigin da kasar Faransa take yi a harkokin kasar Siria a rubuce rubucen da suke rike da su a hannayensu.
-
Faransa Ta Yi Gargdi Akan Bullar Yakin Basasa A Nahiyar Turai
Apr 17, 2018 08:41Shugaban Kasar Faransa ne ya yi gargadin saboda yadda ake kara samun sabani a tsakanin bangarorin nahiyar
-
Macron Da May Sun Fuskanci Fushin 'Yan Majalisun Kasashensu Kan Harin Siriya
Apr 17, 2018 00:32'Yan majalisun kasashen Faransa da Birtaniyya sun tutsiye da kuma nuna fushinsu ga Emmanuel Macro, shugaban kasar Faransan da kuma Theresa May, firayi ministan Birtaniyyan sakamakon harin da suka kai kasar Siriya ba tare da izinin MDD ko kuma alal akalla izinin majalisun kasashen na su ba.
-
Macron Ya Ce Ba Zai Goyi Bayan Hana Sanya Hijabi a Kasar Faransa Ba
Apr 16, 2018 14:29Shugaban kasar Faransa ya bayyana cewa shi ba zai goyi bayan hana sanya hijabi a kasar ba, kuma ya ce wajibi ne a mutunta akida da kuma addinin ko wani dan kasa.
-
Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ya Mai Da Martani Akan Harin Kasar Mali
Apr 16, 2018 07:59Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya ta bakin kakakinsa Stéphane Dujarric ya kira yi dukkanin bangarori rikici a kasar ta Mali da su mai da wukakensu cikin kube, su rungumi sulhu
-
Sharhi: Hari Mai Kama Da Hadarin Kaka Da Amurka Ta Jagoranta Kan Syria
Apr 16, 2018 03:11Jaridar New York Times da ake bugawa a kasar Amurka, ta bayyana mahangarta dangane da harin da Amurka ta jagoranci kaddamarwa a kan Syria, inda kasashen Birtaniya da Faransa suka mara mata baya wajen kai harin da jijjifin safiyar Asabar da ta gabata.
-
OPCW Na Taro Kan Zargin Amfani Da Makami Mai Guda A Siriya
Apr 16, 2018 01:53A wani lokaci a yau Litini ne, hukumar da ke kula da hana bazuwar makamai masu guba (OPCW), za ta yi taro kan zargin amfani da makami mai guda a yankin Duma na kasar Siriya.
-
Isra'ila Ta Sallami Bakin Haure 'Yan Afrika 200
Apr 16, 2018 01:49Sama da bakin haure 'yan Afrika, 200 ne da ake tsare da su a wani gidan yari dake kudancin H.K. Isra'ila aka sallama a jiya Lahadi.
-
Ruhani: Harin Siriya Na Nuni Da Cewa Amurka Tana Da Alaka Kai Tsaye Da 'Yan Ta'adda
Apr 15, 2018 12:54Shugaban kasar Iran Dakta Hasan Ruhani ya bayyana cewar harin da Amurka, Faransa da Birtaniyya suka kai Siriya, wuce gona da iri kana kuma kokari ne na karfafa 'yan ta'adda da zai iya cutar da tafarkin sulhu na siyasa a kasar.