-
Shugaban Kungiyar Ansarullah: Al'ummar Yemen Ba Za Su Meka Wuya Ga Makiya Ba
Sep 21, 2018 02:07Abdulmalik Badruddin al-Huthy Shugaban kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen wanda ya gabatar da jawabi jiya alhamis a Sana'a babban birnin kasar Yemen ya tabbatar da cewa duk da irin kisa da ta'addancin da kawancen saudiya ke yi a kasar ba zai sanya al'ummar kasar ta meka wuya ba.
-
Miliyoyin Al'ummar Musulmi Sun Fara Gudanar Da Juyayin Ashura A Sassa Daban Daban Na Duniya
Sep 20, 2018 02:09Miliyoyin al'ummar musulmi musamman mabiya tafarkin iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka {a.s} sun fara gudanar da juyayi tare da alhinin tunawa da zagayowar ranar Ashura 10 ga watan Muharram, ranar da aka aiwatar da kisan gilla kan jikan fiyayyen halitta Manzon Allah {s.a.w} wato Imam Husaini dan Ali dan Abi-Talib {a.s}.
-
Jami'an Tsaron Iran Sun Dakile Kokarin 'Yan Ta'adda Na Kai Hare-Hare Lokacin Ashura
Oct 10, 2017 02:22Ministan tsaron cikin gida da tattaro bayanan sirri na kasar Iran Sayyid Mahmoud Alawi ya bayyana cewar jami'an tsaron Ma'aikatar tasa sun sami nasarar dakile wani shiri na kai hare-haren ta'addanci a cikin Iran lokacin Ashura yana mai cewa jami'an tsaron sun kame wani adadi na 'yan ta'addan.
-
Juyayin Ashura Ya Game Dukkan Yankunan Kasar Iran A Yau Lahadi
Oct 01, 2017 15:46An gudanar da juyayin ashoora a duk fadin Iran a yau Lahadi wanda yayi dai dai na 10 ga watan Muharram ranar tunawa da shahadar Imam Husain (a) jikan manzon All..(s).
-
Sayyid Nasrallah: Sahyoniyawa Za Su Kwashi Kashinsu A Hannu Matukar Suka Kaddamar Da Yaki Kan Hizbullah
Oct 01, 2017 06:53Shugaban kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon Sayyid Hasan Nasrallah ya ja kunnen haramtacciyar kasar Isra'ila da cewa za su debi kashinsu a hannun matukar gigi ya debe su suka kaddamar da yaki a kan kungiyar Hizbullah yana mai kiran yahudawan da suka yiyo hijira zuwa "Isra'ila" da su gaggauta komawa inda suka fito.
-
'Yan Shi'a Na Gudanar Da Juyayin Ranar Tasu'a A Kasashe Daban-Daban Na Duniya
Sep 30, 2017 07:47Musulmi 'yan Shi'a a duk fadin duniya sun fara gudanar da ranar Tasu'a don tunawa da rana ta tara na watan Muharram rana guda kafin faruwar Waki'ar Karbala inda Imam Husain (a.s) da iyalai da sahabbansa suka yi shahada a Karbala.