Pars Today
Majiyar tsaron Najeriya ta sanar da cewa kungiyar boko haram ta kai wani harin ta'addanci a yankin arewa maso gabashin kasar.
Kamfanin dillancin labarun Faransa ya ambato hukumar da ke kula da 'yan gudun hijira ta MDD tana cewa; Da akwai bukatar dalar Amurka miliyan 160 saboda yan gudun hijirar boko haram
Babban Kwamishinan dake kula da 'yan gudun hijra na MDD ya bukaci taimakon kudi na dala miliyan 160 domin taimakawa 'yan gudun hijrar da rikicin boko haram ya raba da gidajensu a yankin tabkin Chadi.
Ministan sadarwar kasar Somaliya ya sanar da cewa: Jami'an tsaron kasar sun samu nasarar 'yantar da kananan yara 32 daga hannun 'yan ta'addan kungiyar Al-Shabab ta kasar.
Majiyar tsaron Kamaru ta sanar da cewa: 'Yan kungiyar ta'addanci ta Boko Haram sun kaddamar da hare-haren wuce gona da iri kan kauyuka uku da suke shiyar arewacin kasar.
Majiyar watsa labaru mai alaka da gwamnatin hadin kan kasar Libya ta ce; An kama mutumin ne agari Sart, bisa zargin yana safarar 'yan kungiyar Da'esh zuwa kadancin kasar
Majiyar tsaron Kamaru ta sanar da cewa: Wani gungun 'yan bindiga da ake kyautata zaton mayakan kungiyar Boko Haram ne sun kai hare-hare kan yankunan da suke arewacin kasar, inda suka kashe mutane uku.
Majalisar musulinci ta Najeriya reshen jahar Adamawa ta sanar da cewa sama da musulmi dubu 5 ne suka yi shahada sanadiyar hare-haren ta'addanci na kungiyar boko haram.
Ma'aikatar cikin gidan kasar Tunusiya ta sanar da cewa jami'an tsaron kasar sun sami nasarar tarwatsa wata kungiyar 'yan ta'adda ta mutane 9 larduna "Susa" da "Al-Qirawan" da kuma "Manuba" da ke kasar.
Mayakan kungiyar Boko Haram sun kaddamar da wani hari kan sojojin Nigeriya a Kauyen Mainok da ke karamar hukumar Kaga a jihar Borno da ke shiyar arewa maso gabashin kasar da nufin kwace iko da barikin soji.