-
Sayyid Nasrallah: Saudiyya Tana Kokarin Haifar Da Fitina Ne Tsakanin Shi'a Da Sunna
Mar 02, 2016 01:59Shugaban kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon Sayyid Hasan Nasrallah ya bayyana cewar babban abin da kasar Saudiyya ta sa a gaba shi ne haifar da rikici da fitina tsakanin Shi'a da Sunna a yankin Gabas ta tsakiya da sauran yankuna na duniya, yana cewa daga yanzu kungiyar ba za ta yi shiru kan irin danyen aikin da Saudiyya take aikatawa a kasashen musulmi ba